Saurari premier Radio
33 C
Kano
Monday, September 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiYadda kimanin Naira Tirilyan uku suka bace a mulkin Buhari-EFCC

Yadda kimanin Naira Tirilyan uku suka bace a mulkin Buhari-EFCC

Date:

Yadda kimanin Naira Tirilyan uku suka bace a mulkin Buhari-EFCC

Sabon shugaban hukumar EFCC Ola Kayode ya ce Naira tiriliyan biyu da biliyan darI tara ta yi batan dabo lokacin mulkin Buhari.

Ya ce kudaden da aka tsara domin yin muhimmam ayyuka sun bata ne daga shekarar 2018 zuwa 2020.

Mr Kayode ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani gaban zauren majalisar kasar nan.

Ya ce ya gudanar da bincike kan muhimman abubuwa 50, inda ya ce ya gano badakala da aka yi a bangaren bayar da kwangila.

Ya ce a tsakanin shekaru ukun nan ya gano yadda tirilyan biyu da biliyan dari tara ta yi batan dabo.

A cewarsa wadannan kudade da anyi amfani da su yadda ya da ce da kasar nan ta ci gaba yadda ya kamata.

Ya kuma zargi tsohon shugaban EFCC da ya bari wadannan kudade suka salwanta.

Ya ce da kudaden basu salwanta ba za a iya yin titi mai kilo mota 1000, za kuma a iya gina manyan makarantu 200.

Ya kuma ce kudin za a iya ilimantar da dalibai 6,000 tun daga firamare har zuwa jami’a.

A cewarsa kudaden za kuma su isa a gina gidaje 20,000 masu daki uku a fadin kasar nan.

Haka kuma ya ce kudaden za su iya samar da manyan Asibitoci masu daraja ta daya a daukacin jihohin kasar nan.

A cewarsa ya kamata majalisa ta san wannan ta kuma dauki matakin gaggawa a kai domin dakile satar kudin gwamnati.

Latest stories

Related stories

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri...

PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben gwamnan jihar Edo

Jam’iyyar PDP ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman...