Gwamnatin Jihar Kebbi ta sanar cewa za a gudanar da bikin Yawuri Rigata da Al’adu karo na 5 a Yauri daga 4 zuwa 7 ga Fabrairu, 2026.
Shugaban Bikin kuma Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya bayyana haka a taron manema labarai a Birnin Kebbi, yayin da aka kaddamar da shirin taron.
- Kebbi: Gwamnati ta kafa kwamiti bincike kan gobarar da aka samu a wasu makarantu
- Tinubu ya buƙaci jami’an tsaro su killace dazukan jihohin Kwara,Kebbi, Neja
Bikin zai dauki kwanaki hudu, inda za a samu nune-nunen kasuwanci, shirin noma, wasan ruwa, al’adun gargajiya, da babban taron Rigata.
Tafida ya ce kalmar Rigata na nufin yakin ruwa, alama ce ta jarumtaka da kima, wanda ya samo asali shekaru fiye da 200 da suka wuce daga yadda mutanen Gungu ke fafatawa da kifaye masu hadari a Kogin Neja.
Ya kara da cewa bikin na wannan shekara an tsara shi ne domin nuna arzikin al’adu, hada kan al’umma, bunkasa yawon bude ido da tattalin arziki a jihar, tare da godiya ga gwamnan jihar, Dr. Nasir Idris, kan goyon bayan da yake bayarwa.
