Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta kasa ta bullo da wani tsari na amfani da keke na musamman a filayen jirgin wanda zai taimakawa masu lalurar kafa, ko tsofaffi wajen tafiya a filin da nufin saukaka musu zirga zirga.
Hukumar ta ce an tsara samar da keken ne don tabbatar da aminci, da kwanciyar hankali ga dukkan nau’ikan matafiya.
Daraktan Hulda da Jama’a na hukumar, Obiageli Orah, ta bayyana cewa a yanzu za a rika amfani da keken wajen daukar nau’in mutanen don hawa jirigi ko kuma bayan sun sauka.
Ta kara da cewa an samar da kayan aiki da suka hada da dakunan wanka da na lifta don daukar mutanen kasa zuwa sama, a filayen jirgin domin saukaka zirga-zirga.
Orah ta kuma shawarci fasinjojin da ke bukatar tallafi da su sanar da ma’aikatan kamfanin jirginsu ko na filin jirgin sama akan lokaci, ko kuma su gabatar da bukatarsu a teburin taimako na musamman idan sun isa filin.
