Shahararren dan wasan kwallon kafa a Kano, kuma sananne, mai horas da kwallon kafa Kabiru Ali Mazado ya rasu a yau alhamis.
Makusancinsa wanda ya yi dawainiya da shi lokacin da yake fama da rashin Lafiya Ahmad Babandi Gama, ne ya tabbatar da mutuwar Mazado a ganawarsa da Premier Radio.
Kafin rasuwarsa Mazado, ya bayar da gagarumar gudunmawa a fage na kwallon kafa, kuma ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa daban-daban a ciki da wajen jihar Kano.
Kabiru Mazado, kafin rasuwarsa ya shafe akalla watanni takwas ya na fama da rashin Lafiya kamar yadda Ahmad Babandi Gama ya bayyana.
Haka Zalika Marigayi Kabiru Mazado, ya bugawa kungiyoyi kwallon kafa harda Kano Pillars da kuma sauran kungiyoyi a Najeriya.
Babandi Gama, ya ce za a yi jana’izarsa da misalin karfe 1 na ranar Alhamis a gidansu da ke Rigga, Gwagwarwa kusa da L E A ta karamar hukumar Nassarawa.
