Hukumar samar da ruwan famfo a ƙananan hukumomi ta jihar Kano (KASSTOWA), ta buƙaci manajojin cibiyoyin samar da ruwa da shugabannin kwamitocin ruwa da su haɗa kai wajen kawo ƙarshen matsalar ƙarancin ruwan sha da ke addabar wasu al’ummomi a faɗin jihar.
Mukaddashin Shugaban hukumar, Injiniya Sani Bala Danbatta, ne ya yi wannan kira yayin wani taron haɗin gwiwa da manajojin cibiyoyin ruwa da shugabannin kwamitocin.
Danbatta ya bayyana su a matsayin waɗanda ke da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da samun ruwan sha ga al’umma, tare da bukatar su riƙa duba cibiyoyin tace ruwa akai-akai domin tabbatar da ingancin ayyukansu da gano matsalolin da ke buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Haka kuma, ya buƙaci shugabannin kwamitocin da su riƙa sanar da al’ummominsu halin da ake ciki, tare da kare kayayyakin samar da ruwa daga lalacewa da ɓarna.
A nasu ɓangaren, Shugaban ƙungiyar kwamitocin ruwan Alhaji Garba Sa’idu Gwarzo, ya yabawa gwamnatin Kano bisa kafa hukumar, yana mai cewa kawo yanzu ta gudanar da ayyuka daban-daban cikin ɗan lokaci domin inganta samar da ruwan sha a ƙananan hukumomi.
A nasa jawabin, Mukaddashin Mataimakin Manajan Daraktan hukumar, Aminu Yaro, ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta magance matsalolin rashin tsaro da ƙarancin ma’aikata da ke kawo cikas ga gudanar da ayyukanta, tare da jaddada aniyar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na magance matsalar ƙarancin ruwa, wadda ta haifar da kafa hukumar.
