Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa sake lashe zaɓen gwamna a 2027 ba lamari ne na ko a mutu ko a yi rai ba, yana mai cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda Ya so.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin rantsar da sabbin kwamishinoni biyu, Sanusi Bature Dawakin-Tofa da Balarabe Sa’idu Gani, a gidan gwamnatin Kano.
Abba Kabir Yusuf ya ce duk wanda ke kallon siyasa a matsayin abin da dole sai ya samu nasara, ya kamata ya sake tunani, domin mulki na hannun Allah ne.
Ya tuna yadda suka amince da sakamakon zaɓen 2019 duk da rashin nasara, tare da bayyana cewa nasarar da suka samu a 2023, bayan shari’ar da ta kai Kotun Ƙoli, ƙaddarar Allah ce.
Gwamnan ya jaddada cewa makomar zaɓen 2027 na hannun Allah take, kuma babu wanda zai iya bayar da mulki ko hana shi sai da yardarSa.
