Isra’ila ta shirya haramtawa ƙungiyoyin agaji 37 da ke aiki a Gaza da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan gudanar da ayyukansu daga ranar daya ga watan Janairun 2026.
Isra’ila ta ce ƙungoyoyin sun gaza gabatar da cikakken bayanan ma’aikatansu, wanda ta ce yana da matuƙar muhimmanci domin kare yaɗuwar ‘yan ta’adda.
Tuni dai aka dakatar da ayyukan fitattun ƙungiyoyin agaji kamar ActionAid da dai sauransu.
Tuni dai wakilai daga ƙasashe da dama suka yi allawadai da matakin na Isra’ila a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa inda suka ce matakin zai ƙara jefa ayyukan jin ƙai cikin mawuyacin yanayi kamar ayyukan kula da lafiya a Gaza.
