Gwamnatin Jihar Borno ta fara dawo da ‘yan gudun hijira sama da 3,000 da suka tsallaka Kamaru tsawon shekaru fiye da 11 da suka gabata, a wani muhimmin mataki na ƙoƙarin dawo da rayuwar al’umma bayan rikicin da ya daɗe yana addabar yankin.
Matakin na zuwa ne biyo bayan alƙawarin da Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi a ranar 8 ga Disamba, 2025, kamar yadda Shugaban Kwamitin Kula da ’Yan Gudun Hijira na Jihar Borno, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya bayyana.
Wakilbe, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa Kamaru, ya ce sun gana da jami’an gwamnatin Kamaru da kuma wakilan Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNHCR) a sansanin ’yan gudun hijira na Minawao da ke Maroua, inda aka kammala shirye-shiryen dawo da ’yan gudun hijirar cikin tsaro da aminci.
Tawagar ta kuma gana da gwamnan yankin Arewa Mai Nisa na Kamaru, Midjiyawa Bakari, wanda ya yaba wa Gwamnatin Borno bisa ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninta da Kamaru, yana mai bayyana haɗin gwiwar a matsayin muhimmin ginshiƙi na karewa da kuma dawo da waɗanda rikici ya raba da muhallansu na asali.
Dubban ’yan Jihar Borno ne dai suka tsallaka zuwa ƙasar Kamaru a lokacin da rikicin Boko Haram ya tsananta, inda da dama daga cikinsu suka shafe sama da shekaru goma a sansanonin ’yan gudun hijira.
