Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, zai kaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na ƙananan hukumomi 44 na jihar, a ƙaramar hukumar Rogo ranar lahadi mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa an zaɓi Rogo domin fara gangamin ne saboda muhimmancin matsayinta na garin da ke kan iyakar Kano da wata jihar, inda ya buƙaci magoya bayan jam’iyyar, abokan hamayya da sauran al’umma da su kiyaye doka da oda tare da gudanar da ayyukansu cikin lumana.
Gwamna Abba ya kuma yi gargaɗin a gujewa fito da makamai ko duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali, yana mai jaddada cewa ana buƙatar gudanar da gangamin cikin zaman lafiya, ladabi da mutunta juna.
Gwamnan ya kuma buƙaci masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyoyi da su kiyaye dokokin zirga-zirga tare da tuki cikin taka-tsantsan domin kaucewa haɗurra yayin gudanar da ayyukan gangamin.
Gwamnan ya a duk ƙaramar hukumar da zai ziyarta, za’a ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa, duba ayyukan da ake kan gudanarwa ko aza harsashin sababbin ayyuka, domin nuna irin ayyukan da gwamnatinsa ke aiwatarwa.
