Asusun Tallafawa Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya jinjinawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa daukar nauyin samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara masu fama da lalurar Tamowa a jihar.
Shugaban UNICEF Mista Rahama Rihood Farah, ne ya bayyana haka a yayin ziyarar jaje da Daraktar Hukumar Kiyaye Jin Kai ta kai wa Shugaban a Kano.
Mista Farah ya bayyana matakin Gwamna Abba a matsayin wani bangare na kula da dubban rayukan kananan yara, wajen samar musu da hanyoyin inganta lafiyarsu.
A nata jawabin, Shugaban Hukumar Kula Da Kula da kuma Kare Walwalar Jama’a (KASPA) Fateema Abubakar Abdullahi, ta mika godiyar ta ga Gwamnan Kano da kuma UNICEF bisa gudummawar da suka dade suna bayarwa, musamman wajen samar da kariya ga Jama’a, da kuma tallafi a bangaren ilimi da abinci mai gina jiki da kare hakkin yara.
Hajiya Fateema ta kuma nemi karin hadin gwiwa da UNICEF a fannoni da suka hada da karfafa cibiyoyin gwamnati, mayar da yara makaranta wadanda suke gararamba a titi, da kuma ci gaba da aiki tare a dukkan bangarorin da UNICEF ke gudanarwa.
