Ƙungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya, IPMAN, ta ce tana duba yiwuwar sake daidaita farashin man fetur a kasuwannin ƙasar, sakamakon sauye-sauyen da ake samu a farashin man da ake saya daga matatun mai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwar man fetur ke fuskantar rashin tabbas, yayin da wasu dillalai suka dakatar da sayen sabon kaya saboda yawan sauye-sauyen farashin da ake samu daga cibiyoyin ajiyar man fetur.
IPMAN ta yi gargadin cewa idan wannan yanayi ya ci gaba, akwai yiwuwar farashin man fetur ya ƙara tashi.
Ƙungiyar ta yi kira da a ƙara mayar da hankali kan man fetur da ake tacewa a cikin gida, tana mai cewa farashin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ya fi na man da ake tacewa a Matatar Man Fetur ta Dangote.
IPMAN ta ce sauye-sauyen farashin na buƙatar ingantaccen tsari da kuma samar da kyakkyawar manufa, domin kare dillalai daga asara tare da rage yiwuwar ƙaruwar farashin.
