Gwamnatin tarayya ta ce akwai kyakkyawar fahimtar juna tsakaninta da kasar Amurka kan batun yaki da ta’addanci da inganta tsaro.
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne, ya bayyana haka bayan ganawarsa da mataimakiyar sakataren harkokin siyasa ta Amurka, Allison Hooker, a Abuja.
Ribadu ya ce kasashen biyu sun mayar da hankali kan kare ‘yancin addini da kuma magance matsalolin tsaro da ke addabar wasu yankunan Najeriya.
Ya kara da cewa ganawar ta kuma duba ci gaban hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan shugaba Donald Trump mulki.
Najeriya ta ce za ta kara aiki tare da jami’an tsaron Amurka domin karfafa yaki da ta’addanci, bunkasa dabarun tsaro da kare rayukan fararen hula.
