Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da su guji amfani da kalaman tunzuri da za su iya haddasa rikici gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sani-Omolori Aliyu, ne ya yi wannan gargaɗi yayin ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar rundunar da ke Bauchi, wanda mataimakin kwamishinan ’yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Abdulmajid Isah, ya wakilta.
Kwamishinan ya buƙaci jam’iyyun siyasar da su mayar da hankali kan manufofinsu da alkawuran da suke yi wa al’umma, maimakon yin amfani da kalaman batanci da sukar abokan hamayyarsu.
Rundunar ta kuma tabbatar wa jam’iyyun cewa za ta gudanar da aikinta na samar da tsaro cikin adalci da ƙwarewa, ba tare da nuna bambanci ga wata jam’iyya ba.
Haka kuma, rundunar ta yi kira ga shugabannin siyasa da su wayar da kan magoya bayansu kan muhimmancin zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai yayin da zaɓen 2027 ke ƙara gabatowa.
