Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta gayyaci bangarorin dake rikici da juna kan batun shugabancin jam’iyyar ta PDP, wanda kuma ake ganin rikicin na ci gaba da mayar da jam’iyyar koma baya.
Shugaban hukumar ta INEC shi ne ya gayyaci bangarorin guda biyu, wadanda suka hadar da bangaren Kabiru Tanimu Turaki SAN, da mambobin kwamitin zartarwa na jam’iyyar ta PDP wadanda zaba a kwana nan, tare da bangaren ministan birnin tarayyar Abuja Nyesom Wike karkashin jagorancin Alhaji Abdulrahman Mohammed.
Ganawar ta gudana ne a hedikwatar hukumar ta INEC dake birnin tarayyar Abuja, wanda kuma a cewar sa hukumar ta yanke shawarar shiga cikin wannan batun ne biyo bayan jerin korafe korafe data karba kan halin da jamiyyar ke ciki a yanzu haka.
- Shugaban INEC Ya Mika Ragamar Hukumar ga Shugabar riko
- INEC ta bada takardar shaidar cin zabe ga mutanen da suka lashe zaben cike gurbi a Kano
- INEC Ta Gargadi ‘Yan Siyasa Da Su Kaucewa Yakin Neman Zaben 2027
Ya kara da cewa, a yanzu haka hukumar ta INEC tana da ci gaba da shirye shiryan gudunar da wani zabe a birnin tarayya Abuja da kuma zaben gwamnoni a jihohin Ekiti da kuma Osun a shekarar 2026 mai zuwa.
Hukumar INEC tace tana gudunar da aiyukan ne bisa tanadin dokokin domin ganin tayi wa ko wane bangare adalachi don samar da zaman lafiya.
