Gwamnatin tarayya ta ba ‘yan kasuwar Singa gudunmawar Naira Biliyan 5 a matsayin tallafi.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar gani da ido da ya kai kasuwar a ranar Litinin.
A jawabinsa yayin ziyarar, Shettima ya jajantawa ‘yan kasuwar da iftila’in gobara ta afkawa da kuma gwamnati da sauran al’ummar jihar.
Shettima ya kuma bayyana gudunmawar gwamnonin APC na Naira biliyan uku ga ‘yan kasuwar.
A yayin ziyarar Shettima ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnatin tarayya da na jihar Kano da gwamnonin jihohin Kebbi da Katsina da Sakkwato da sauransu.
