Hukumar Kula da Hana Safarar Mutane ta kasa, NAPTIP ta jaddada kudirin hukumar na hada kai da kasashen waje wajen yaki da safarar mutane da kuma kare ‘yan Najeriya da abin ya shafa a kasashen waje.
Daraktar hukumar, Binta Adamu Bello ce ta bayyana hakan yayin karbar bakuncin tawagar kasashen Cabo Verde, wadda ta kunshi jami’an Hukumar Gudanar da Hijira da Ofishin Kula da Safarar Mutane na kasar.
Tawagar ta samu jagorancin Mr. Omaru Djalo Abreu, Manajan Ayyuka a Cibiyar Duniya kan Manufofin Gudanar da Hijira (ICMPD) a Cabo Verde.
- NAPTIP A Kano Ta Kama Mai Tura Mata Aikatau Zuwa Saudiyya
- Saudiyya Ta Zartar da Hukuncin Kisa Kan Mutane 347 A 2025
Bello ta bayyana cewa safarar mutane babbar matsala ce ta duniya da ke shafar kowane jinsi da nahiyar duniya, tana mai jaddada mahimmancin hadin kai tsakanin kasa da kasa.
Mr. Abreu ya ce ziyarar na nufin fahimtar tsarin aiki na NAPTIP, koya kyawawan dabaru, da kuma kafa dangantaka mai dorewa wajen hada kai a nan gaba.
