Ahmad Hamisu Gwale
Neymar Jnr, wanda a yanzu ke bugawa Al-Hilal ta Saudiyya, ya ce ko kaɗan bai yi da-na-sanin zaɓar ƙungiyar Barcelona ba, duk da a lokacin Real Madrid ma ta yi zawarcinsa.
Neymar ya bayyana haka ne a cikin wata hira da fitaccen ɗan jaridan wasanni, Fabrizio Romano.
na kalato daga zantawar ɗanwasan da tsohon ɗanwasan Brazil, Romario.
Da yake ƙara haske kan abin da ya faru a lokacin da Barcelona da Real Madrid suka yi zawarcinsa a tare, sai ya ce kwanaki ne da ba zai taɓa mantawa.
Neymar ya ƙara da cewa lamarin ya jefa shi a ruɗu, amma a ƙarshe, sai ya zaɓi Barcelona saboda zuciyarsa ta fi kwantawa da ita.
