
Wani rahoto na asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya tona asirin yadda ake ci gaba da cin zarafin yara a Najeriya, tare da gargaɗi kan tsananin barazanar da hakan ke yi wa rayuwar su.
A cewar rahoton da UNICEF ta fitar a ranar Litinin, har yanzu akwai dubban yara da ke tsare a hannun hukumomi ba tare da bayani ga iyalansu ba, wasu kuma babu wani tabbaci kan inda suke ko halin da suke ciki.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce cin zarafin yara ta hanyar tsare su ba bisa ƙa’ida ba, shari’a marar adalci, da rashin kariya daga doka ya zama abin damuwa a Najeriya. Hakan, a cewar rahoton, na jefa yara cikin tsananin fargaba da rashin makoma.
Rahoton ya nuna cewa tsakanin 2018 zuwa 2022, an gano cewa mutane sama da 87, da ƙananan yara 1,279, na tsare a gidajen yari ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ko yanke musu hukunci ba.
Wasu daga cikinsu sun shafe fiye da shekaru biyar a tsare.
UNICEF ta bayyana cewa rashin isassun kotuna da kuma cibiyoyin kula da yara masu laifi na daga cikin manyan matsalolin da ke haifar da wannan bala’i.