Shugaban kasa bola Tunubu ya aike da tawaga ta musamman a madadin gwamnatin tarayya zuwa jihar Neja domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bayan iftila’in ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Mokwa.
Tawagar ta shugaban kasar ta hada da ministan yada labarai da wayar da kan Alumma Mohammed Idris da takwaransa na ma’aikatar jin kai da yaki da talauci Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda.
A yayin ziyarar da suka kaiwa mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba a ranar Asabar a Minna, ministan yada labarai Mista Idris, ya mika sakon ta’aziyyar shugaba Tinubu ga gwamnati da al’ummar jihar kan ibtila’in ambaliyar ruwan.
Ministan ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya umarci hukumar wayar da kan jama’a ta kasa (NOA) da ta hada kai da gwamnatocin jihohi a fadin kasar nan don kara kaimi wajen wayar da kan jama’a, musamman ga wadanda ke kusa da kogi ko matattar ruwa domin tabbatar da cewa mazauna yankunan sun bi matakan kariya.
A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, ya godewa gwamnatin tarayya bisa gaggauwa da kuma kai agajin jin kai da ta yi don shawo kan iftilain ambaliyar ruwan, yana mai bayyana jindadinsa game da jajircewar gwamnatin tarayya wajen kyautata rayuwar ‘yan kasa a lokuta da dama
