
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da fitar da ƙarin Naira biliyan 6 domin biyan haƙƙin ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma iyalan waɗanda suka rasu daga aikin gwamnati.
Mai Ba Gwamna Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ibrahim Adam ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
“ƙarin kuɗi na daga cikin bashin Naira biliyan 21 da gwamnatin ke biya wanda ta gada daga gwamnatin Ganduje”. In ji shi.
Ya kuma kara da cewa, wannan shi ne karo na huɗu da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke fitar da kuɗaɗen don biyan bashin wadanda suka yi ritya tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023.
Sanann ya kuma ce, Gaba ɗaya bashin fansho da gwamnatin Abba ta gada daga shekarar 2024 ya kai Naira biliyan 48 da miliyan 106, wanda yanzu haka gwamnatin ta biya Naira biliyan 27 cikin jimillar.