Babban Daraktan rukunin Kamfanin Gerawa Alhaji Ibrahim Muhammad yayi kira ga gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya da su haɗa kai tare da ajiye bambancin siyasa domin samar da tsare-tsaren da zasu bunƙasa harkar noma, ƙarfafa masana’antu, dan wadatar abinci ga al’ummar yankin da ƙasa baki ɗaya.
Gerawa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce
noma shine ginshiƙin tattalin arzikin Arewa don haka akwai buƙatar shugabannin jihohin yankin su haɗa ƙarfi wajen samar da manufofin da za su taimakawa manoma, rage matsalolin da suke fuskanta, da kuma ƙara yawan amfanin gona.
A cewarsa, haɗin kan gwamnonin zai taimaka wajen samar da ingantattun shirye-shiryen da zasu ba manoma damar samun takin zamani, iri masu inganci, magungunan kashe kwari da kuma hanyoyin samun rance cikin sauƙi domin bunƙasa harkokin noma.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda manoma da dama suka fuskanci ƙalubale a cikin shekaru biyu da suka gabata, inda wasu daga cikinsu suka kasa samun ribar da ta dace daga ayyukansu sakamakon tsadar kayan noma da sauye-sauyen kasuwa.
Ya yi gargadin cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba wajen tallafa wa manoma da ƙarfafa harkokin noma, Najeriya na iya fuskantar matsalar ƙarancin abinci a nan gaba, lamarin da zai ƙara jefa al’umma cikin wahalar rayuwa.
