
Aminu Abdullahi Ibrahim
Majalisar wakilan ƙasar nan na nazarin wani kudirin doka da zai tilasta wa direbobin manyan motoci da tankokin mai yin gwajin miyagun ƙwayoyi duk bayan watanni shida, domin rage yawan haɗurra a manyan hanyoyin Najeriya.
Wanda ya gabatar da kudirin, ɗan majalisa Peter Uzokwe, ya ce amfani da miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa haɗurran manyan motoci.
Ya ce ko da direba ya kware, idan ƙwayoyi suka fara tasiri a jikinsa, zai rasa ikon tuki yadda ya kamata.
Uzokwe ya bayyana hakan ne a wani zaman tattaunawa tsakanin kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da albarkatun man fetur da ƙungiyoyin masu kasuwancin man fetur, ciki har da DAPPMAN, MEMAN, da IPMAN.
A zaman, masu kasuwancin sun kuma yi kira ga gwamnati da ta inganta manufofin da za su sauƙaƙa kasuwanci, inganta tace mai a gida da kuma magance matsalolin sufuri.
Idan kudirin ya zama doka, za a riƙa yi wa direbobin manyan motoci gwajin miyagun ƙwayoyi sau biyu a shekara, a matsayin wani mataki na inganta tsaron hanyoyi da rage haɗurran tankokin mai da tireloli.
