Sace ‘yan mata dalibai da ‘yan ta’adda suka yi nuni ne ga gazawar wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Amnesty International ce ta bayyan hakan a sanarwar da ta fitar na Allah-wadai kan sace dalibai mata 25 da ’yan bindiga suka yi a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Maga a Jihar Kebbi.
“Wannan hari na sake nuna yadda Gwamnatin Najeriya ke gazawa wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu, musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
“Muna kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen tabbatar da ganin an kubutar da daliban cikin koshin lafiya”. In ji kungiyar.
Kungiyar ta kuma bukaci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda ke da hannu a kai, tare da kawo ƙarshen yawan sace-sacen da suka zama barazana ga ilimi da makomar ’yan makaranta a jihar.
