Wata tawagar magoya bayan tsohon mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ta kai ziyarar nuna goyon baya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen ficewarsu daga jam’iyyar NDC zuwa APC.
Mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
A cewar sanarwar, tawagar karkashin jagorancin makusancin Gawuna Muhammad Badaru Umar, ta kunshi wasu manyan ’yan siyasa ciki har da Mataimakin Shugaban NDC na Kano, Ali Datti Yako, Mansur Isa Gawuna da Uba Tanko Mijinyawa, da sauran jiga-jigan siyasar Kano.
Da yake magana yayin ziyarar, Muhammad Badaru Umar ya ce sun yanke shawarar ganawa da Gwamna Abba Kabir Yusuf ne saboda kishinsu na ganin an samu ci gaba da bunkasa Kano, tare da bayyana cewa ziyarar wani bangare ne na shawarwarin da suke yi kan makomar siyasar Kano.
Shi ma Ali Datti Yako ya ce al’ummar Kano na sane da kokarin da Gwamna Abba ke yi wajen sauya fasalin jihar da inganta rayuwar jama’a.
Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kano gabanin babban zaben 2027, inda manyan ’yan siyasa ke sake duba matsayinsu da alakar siyasarsu.
