Gwamnatin Jihar Kano ta sake yin kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sakin tallafin Naira biliyan 5 da aka yi alƙawarin bai wa ’yan Kasuwar Singa domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da ƙoƙarin tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta yi alƙawarin bayar da wannan tallafi bayan gobarar da ta lalata dukiyoyi na miliyoyin naira a Kasuwar Singa a farkon shekarar 2023.
Sai dai, ya ce duk da wannan alƙawari, har yanzu ba a saki kuɗaɗen tallafin ba, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ke sake roƙon Gwamnatin Tarayya da ta cika alƙawarin domin taimaka wa ’yan kasuwar da abin ya shafa.
