
Gwamnan Kano a yayin ziyarar inda gobarar ta yi barna a unguwar Dakata
Daga Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba su tallafin Naira Miliyan 100 da alkawarin kafa asusun taimaka musu da kuma tare da mayar da kasuwar ta zamani
Gwamnan Kano ya jajanta wa wadanda iftila’in gobara ta shafa a rukunin masana’antu na Dakata dake Karamar Hukumar Nassarawa a jihar.
Ya jajanta musu ne a yayin wata ziyara gani da ido da ya kai kasuwar a ranar Asabar.
A jawabinsa, gwamnan ya bayyana irin muhimmancin kasuwar ga tattalin arzikin jihar Kano da kuma samar da aikin yi musamman ga matasa.
“Kasuwar tana taimaka wa wajen bunƙasa tattalin arzikin Kano da kuma magance zaman kashe wando a tsakanin matasa… A madadin Gwamnati da kuma al’ummar Kano ina jajanta wa ‘yan kasuwar dangane da wannan gobara.
“Gwamnatin Kano ta ba ku tallafin Naira miliyan 100 kuma za a sanya mu ku wutar Solar. In ji shi.
Sannan gwamnan ya yi kira ga manyan mutane da ‘yan kasuwar Kano da kuma na Najeriya da su tallafawa wadanda gobarar ta shafa domin suna bukatar a tallafa musu ba wai iya jajantawa a jaridu ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya kuma bayar da umarnin share kasuwar ta yadda za a yi saurin farfado da kamfanoni da injinan da suka kone.
Sannan kuma za a yi taswira domin mayar da gurin na zamani ta yadda ba za a kara samun makamanciyar gobarar ba.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin bude asusu ga wadanda suke son tallafawa mutanen dake rukunin kananan masana’antun na unguwar Dakata.