Hukumar da ke kula da jami’o’i ta ƙasa NUC ta bai wa jami’ar Al-Istiqama Sumaila, Kano cikakken izinin gudanar da shirye-shirye 11, a wani gagarumin ci gaba da ke nuna ingancin koyarwa da tsarin ilimi na jami’ar.
A cewar rahoton NUC, an tantance kwasa-kwasan ne bisa ƙa’idojin “Core Curriculum and Minimum Academic Standards” (CCMAS), inda ya mayar da hankali kan ingancin manhaja, ƙwarewar malamai, kayayyakin koyarwa, da kuma martabar ɗakunan gwaje-gwaje.
Haka kuma, wannan nasara na nufin cewa dukkan Kwasa Kwasan sun samu amincewa na tsawon shekaru biyar, wanda ke ƙara tabbatar da ingancin takardun shaidar da jami’ar ke bayarwa.
Mahukuntan jami’ar sun miƙa godiya ta musamman ga wanda ya kafa jami’ar, Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila, tare da majalisar gudanarwa, shugabannin sassa, malamai, ma’aikata da ɗalibai bisa gudunmawar da suka bayar wajen cimma wannan nasara.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Jami’a, Abdulhadi Sale Kumurya, ya jaddada cewa jami’ar za ta ci gaba da ɗaukar matakan inganta ilimi domin dorewa da kuma ƙara samun irin wadannan nasarori a nan gaba.
