Majalisar dokokin jihar Kano ta ce babu wani batu a hukumance da aka gabatar a gabanta dangane da shirin sauke mataimakin gwamnan.kano Aminu Abdusalam Gwarzo
Mai magana da yawun majalisar, Kamal Shawai, yayin zantawarsa da premier radio ya bayyana hakan boyo bayan jita – jitar da ake yadawa Kan majalisar dokokin kano tana cigaba da tattaunawa a tsakanin ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnan kan yiwuwar fara shirin sauke mataimakin gwamnan idan ya ki yin murabus da kansa.
Shawai ya Kara da cewa zantukan da suke ta yawo a Gari shadi Fadi ne Duba da majalisar ta tafi hutu a halin yanzu, kuma ba za ta dawo zamanta ba sai a watan Fabrairun 2026.
- Gwamnan Kano ya amince da sabbin naɗe-naɗe da ƙarin girma ga wasu jami’an gwamnati
- Gwamnan Kano Ya Taya Premier Radio Murnar Cika Shekaru 4
Kazalika Game da batun baiwa mataimakin gwamnan Aminu Abdusalam Gwarzo wa’adin kwanki biyu ya sauka daga kujerarsa yace majalisar bata da masaniya
Binta Khalid Mohd ta rawaito cewa Kamal Shawai ya bayyana cewa ko da yake ‘yan majalisa sun tattauna batutuwan da suka shafi sauya shekar gwamnan a tsakaninsu ba a hukumance ba, babu wata takarda ko kuduri da aka gabatar wa majalisar dangane da neman mataimakin gwamnan ya sauka ko a saukeshi.
