Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da aka samu da laifin kisan wata dattijuwa, Dahare Abubakar, mai shekaru 67, bisa zargin ta da maita.
Wadanda hukuncin ya shafa sun hada da Da’Luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu, da Ayuba Abdulrahman.
Mai shari’a Usman Na’abba, ya ce kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, wanda ya tabbatar da cewa sun aikata laifin a kauyen Dadin Kowa da ke karamar hukumar Wudil, ranar 15 ga Nuwamba, 2023.
Sai dai kotun ta wanke Nabi’a Ibrahim bayan tabbatar da cewa ba ta gurin da aka aikata laifin.