Rundunar Ƴansandan Jihar Kaduna ta musanta rahotannin da ke yawo na cewa an sace wasu mabiya addinin Kirista 163 a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.
Kwamishinan Ƴansandan Jihar, Muhammadu Rabi’u, ya tabbatar da hakan yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ƙalubalanci duk wanda ke iƙirarin sace mutanen da ya gabatar da hujjoji tare da cikakken jerin sunayen waɗanda ake zargin an sace.
A nasa bangaren, Shugaban Ƙaramar Hukumar Kajuru, Dauda Madaki, ya ce bayan yaɗuwar labarin, ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa Kurmin Wali, yankin da aka ce an sace mutanen, amma binciken da suka gudanar ya nuna cewa labarin ba gaskiya ba ne.
Rahoton sace mutanen ya fara yawo ne da yammacin jiya Litinin, inda ake iƙirarin cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan wasu majami’u biyu a jihar Kaduna, tare da awon gaba da wasu mabiya addinin kirista aƙalla mutane 163.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen Arewa, Reverend Joseph Hayab, yana cewa sun samu bayanai da ke nuna cewa harin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka tilasta wa masu bautar tserewa zuwa cikin daji.
A cewar AFP, Hayab ya ƙara da cewa da fari an sace mutane 172, amma daga bisani mutum tara sun samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane.
