Mayaƙan Boko Haram sun kashe wani fasto tare da mafarauta biyu da wasu ’yan gari a ƙauyen Tarfa da ke Ƙaramar Hukumar Biu a jihar.
Shugaban mafarauta da ’yan sa-kai na Arewa maso Gabas, Malam Shawulu Yohanna, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba da misalin karfe hudu na yamma.
“Abin bakin ciki ne cewa wasu ’yan ta’adda sun kutsa ƙauyen Tarfa na Biu a ranar Laraba. Mafarauta biyu sun rasa rayukansu, da wani Fasto na cocin Ekklesiyar ’Yan Uwa a Najeriya (E.Y.N), da kuma wasu ’yan gari biyu,” in ji shi.
Ya ce mafarauta shida ƙarƙashin jagorancinsa sun yi ƙoƙarin daƙile harin, amma sun kasa jure ƙarfin makaman ’yan ta’addan.
- Sojoji Sun Cafke ’Yan Boko Haram da Bama-Bamai a Borno
- Boko Haram Ta Sanya Sunana Cikin Jerin Wadanda Take Shirin Kashewa- -SHEIK GUMI
Malam Shawulu ya ƙara da cewa maharan sun afka ƙauyen ne lokacin da jama’a suka dawo daga gona domin girbe amfanin gona.
“Faston da aka kashe ya dawo daga gonarsa da misalin karfe hudu na yamma. Da ya ji ƙarar harbe-harbe sai ya fito daga gidansa cikin firgici, nan take ’yan ta’addan suka harbe shi har lahira,” in ji Yohanna.
Jaridar aminiya ta rawaito cewa anyi Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sanda a Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, bai samu ba, domin wayarsa ba ta shiga ba, kuma saƙonnin da aka tura masa bai amsa ba.
