Aƙalla mutane sama da 20 ’yan bindiga suka yi garkuwa da su bayan sun kai hari ƙauyen Gidan Sarki da ke yankin Tuge a Ƙaramar Hukumar Musawa ta Jihar Katsina.
Wani masani kan tsaro mai suna Bakatsine ne ya bayyana hakan a shafinsa X a ranar Talata.
A cewarsa, ’yan bindigar sun shiga ƙauyen, sun harbi wasu mutane, sun kwashe dabbobi, sannan suka sanya firgici a zukatan jama’a.
Wannan ya sa mutane da dama suka gudu suka bar gidajensu.
A halin yanzu, wasu suna kwana a dazuka, maƙabartu, rijiyoyin da aka daina amfani da su, saman rufin gidaje, da kuma ƙarƙashin bishiyoyi saboda tsoron kada ’yan bindigar su sake dawowa.
Bakatsine ya ce lamarin ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a baya tsakanin shugabannin ƙaramar hukumar da ’yan bindigar da ke yankin.
Kawo yanzu, hukumomin tsaro da gwamnatin Jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, yayin da mazauna yankin ke ci gaba da tantance asarar da suka yi.
