Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi zargin kungiyoyi ‘yan bindiga da kuma dakarun gwamnatoci a yammacin Afrika da tafka ta’asa ba tare da daukar wani mataki ba a shekara ta 2024.
A rahoton da ta fitar na sabuwar shekara, kungiyar ta Human Rights Watch ta ce dubban mutane sun rasu wadansu kuma an ji musu raunuka amma kuma ba a dauki hukunci ba.
Kungiyar ta ce, a shekarar ta da wuce ta yi nazari kan cin zarafin bil adama a kasashe fiye da 100 a duniya, abin da ya ba ta damar fitar da wannan rahoton.
Rahoton, mai shafi 546 ya nuna cewa a kasashe da dama gwamnatoci sun murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo.
An kuma kama mutane ba tare da sun aikata laifi ba.
Haka nan an kuma garkame abokan hamayya na siyasa a kurkuku tare da cin zarfin ‘yan jarida da kuma masu rajin kare hakkin bil’adama.
Kungiyar ta ce, ƴan bindiga da sojojin gwamnati sun kashe fararen hula babu gaira babu dalili.
Wadansu mutanen kuma an raba su da muhallansu.
A cewarta, a kasashe fiye da 70 a 2024 da aka gudanar da zabe, shugabanni masu kama karya sun kara karfi tare da kafa dokoki na zalunci.
A Najeriya kuwa rahoton ya ce, akwai rauni game da irin matakan da gwamnati ke dauka wajen hukunci ‘yan bindiga saboda yadda suka raba miliyoyin mutane da muhallansu tare da kashe daruruwan mutane.
Kungiyar ta human rights watch ta ce, sauye-sauyen tattalin arziki a kasar nan sun jawo mummunan talaucin da ba a taba gani ba a cikin shekaru 30 kuma babu wani tsari na hakika da gwamnati ta dauka domin magance matsalar, sai ma ta yi amfani da karfin da ya wuce kima wajen hana zanga-zangar tsadar rayuwa.
