Wani masanin kimiyya ɗan Najeriya, Mubarak Mahmud, wanda ke aiki a ƙasar France, ya jagoranci wani bincike da ya gano sabuwar hanyar da za ta taimaka wa tsirrai su riƙa samun wani muhimmin sinadari daga cikin iska domin bunƙasa girma.
Dr. Mubarak, wanda ɗan asalin Jihar Kano ne, yana gudanar da binciken ne a French National Research Institute for Agriculture, Food and Environment tare da haɗin gwiwar Université Bourgogne Europe da ke birnin Dijon.
A cewarsa, sinadarin da tsirrai ke buƙata domin girma yana da yawa a cikin iska, amma yawancin amfanin gona kamar masara, alkama da shinkafa ba sa iya amfani da shi kai tsaye. Wannan ne ya sa manoma ke yawan amfani da takin zamani domin ƙara wannan sinadari a cikin ƙasa.
Sai dai masana sun ce amfani da takin zamani na da tsada ga manoma, kuma yana iya haifar da matsalolin muhalli kamar gurɓacewar ruwa da kuma hayakin da ke taimakawa dumamar yanayi.
Sabon binciken da Dr. Mubarak ke jagoranta ya mayar da hankali ne kan yadda wasu ƙananan halittu da ke cikin ƙasa za su iya taimaka wa tsirrai su amfana da wannan sinadari daga iska ta hanyar tsarin halittu na dabi’a.
Binciken ya kuma yi nazari kan dangantakar da ke tsakanin tsirrai da wasu fungi masu anfani da ake kira Arbuscular Mycorrhizal Fungi, waɗanda ke shiga cikin tushen tsirrai su taimaka musu wajen shan sinadarai daga ƙasa.
A cewar masanin, waɗannan fungi suna gina wata hanyar sadarwa a cikin ƙasa wacce ke aiki kamar gada tsakanin tushen tsirrai da sauran abubuwan da ke cikin ƙasa.
Haka kuma akwai wasu ƙwayoyin halitta da ke iya ɗaukar wannan sinadari daga iska su maida shi wani nau’i da tsirrai za su iya amfani da shi. Amma sau da yawa sinadarin kan ɓace kafin tsirrai su samu damar amfani da shi.
Saboda haka sabon binciken yana ƙoƙarin haɗa aikin waɗannan ƙwayoyin halitta da kuma fungi domin sinadarin ya riƙa isa kai tsaye zuwa ga tsirrai.
A cewarsa, wannan fasaha ba ta haɗa da sauya ƙwayoyin halittar tsirrai ba, sai dai tana ƙarfafa tsarin dabi’ar da tuni ke faruwa a cikin ƙasa.
Masu binciken sun ce idan wannan fasaha ta yi nasara a gwaje-gwajen gona, za ta iya taimakawa wajen:
ƙara yawan amfanin gona
rage amfani da takin zamani
rage kuɗin noma ga manoma
da kuma kare muhalli.
Sai dai Dr. Mubarak ya jaddada cewa wannan fasaha ba za ta maye gurbin takin zamani gaba ɗaya nan take ba, amma za ta iya zama wata hanya da za ta taimaka wajen inganta dorewar noma a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga masana kimiyya daga fannoni daban-daban su haɗa kai domin ci gaba da bunƙasa wannan bincike, domin inganta yadda tsirrai ke samun abincinsu cikin hanya mai sauƙi, mai inganci da kuma mai dorewa.
