Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da kisan gilla da ’yan ta’adda suka ƙone mutane hudu da ransu a gidajensu a ƙauyen Gwargwabe da ke yankin Nahuce a Ƙaramar Hukumar Bungudu.
Gwamna Dauda Lawal ya halarci sallar jana’iza tare da binne waɗanda abin ya rutsa da su.
A jawabin da ya yi ta bakin mataimakinsa, Mani Malam Mummuni, Gwamna Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ɗaukar duk matakan da suka dace domin kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.
Mataimakin gwamnan ya roƙi al’ummar yankin da su ɗauki lamarin a matsayin ƙaddara, tare da tabbatar musu cewa gwamnati na binciken jinkirin da aka samu wajen isowar jami’an tsaro bayan an sanar da harin.
- ‘Yan ta’adda sun sace dalibai 25 sun hallaka shugaban makaranta a Kebbi
- Harin ‘yan ta’adda: Shugaban Ƙaramar Hukumar Shanono Yajinjinawa Jami’an Tsaro
Ya kuma sanar da kafa sansanin soja a Gwargwabe domin daƙile hare-haren gaba, tare da kira ga al’umma da su ba jami’an tsaro haɗin kai da goyon baya.
Gwamnati ta tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa da buhunan hatsi 100 da kuma tallafin kuɗi na Naira miliyan goma domin rage raɗaɗin da suka shiga.
Harin ya faru ne da yammacin Alhamis, kafin sallar Magriba, lokacin da ’yan ta’adda suka mamaye ƙauyen, suka ƙona gidaje da rumbunan abinci, tare da kashe mutane huɗu — maza uku da mace ɗaya — da kuma dabbobi da dama.
