
Kungiyar Arewa Social Contract, mai rajin tabbatar da adalci a Najeriya ta jaddada goyon baya ga matatar mai ta Dangote, tare da jan kunne ga masu yunkurin kawo cikas ga aikin matatar man.
Wannan na zuwa ne daidadi lokacin da ake ta takaddama tsakanin matatar man da kungiyar ma’aikatan man fetur wato PENGASSAN.
Da yake tattaunawa da manema labarai a Kano, Mai magana da yawun kungiyar Arewa Social Contract kwamared Sani Yusuf Adamu ya bayyana cewa wasu marasa kishin kasa na amfani da kungiyar PENGASSAN domin kawo koma baya ga yunkurin Alhaji Aliko Dangote na wadata Najeriya da man fetur.
Ya kara da cewa matukar gwamnatin ta biyewa kungiyar PENGASSAN wajen daina bawa matatar mai ta Dangote danyen man fetur, to ba shakka hakan zai jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
A cewar Sani Yusuf Adamu kamfanin Mai na Dangote na da alhakin kare ma’aikatansa tare da ƙara samar da dama ga ƴan ƙasa, ba wai ragewa ko sauya su da baƙin haure ba.
Kungiyar ta Arewa Social Contract ta jaddada goyon baya ga matatar mai ta Dangote, tare da jan kunne ga masu yunkurin kawo cikas ga aikin matatar man.