
Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya bayyana zunuban gwamnatin Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ya fi ladanta yawa musamman yadda ta karbo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasashen waje ba tare da bayyana yadda aka yi da kuɗaɗen ba.
Tsohon Sakataren gwamnatin bayyana hakan ne a karkashin wata ƙungiya ta jam’iyyar APC mai suna ‘APC Patriotic Volunteers’ a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba a Kano.
“Kungiyar na da hujjoji daga Ofishin Kula Da Basuka Na Kasa (DMO) da ke nuna cewa gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ta karɓi bashin kasashen waje a cikin shekaru biyun da suka gabata.
“Kuma duk da karɓar bashin, gwamnatin ta sake karɓar kuɗade daga wasu hanyoyi, amma babu wani abin da za a iya gani da ke nuna inda kudaden suka tafi”. In ji shi.
Alhaji Usman ya kuma kalubalanci gwamnatin jihar da ta tabbatar da ikirarin gaskiya da bayyana cikakken bayanin bashin da ke kan jihar a halin yanzu.
Ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatin Gwamna Abba da almubazzaranci da kuɗin asusun kula da muhallin da gwamnatin tarayya ta fitar, waɗanda suka kai Naira biliyan 5.1.