
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, ya karyata zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Kasar nan.
Sarkin ya bayyana hakan ne a babban taron Babban Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Birnin Kebbi a ranar Talata.
“Wannan ikirari ƙarya ne kuma bai kamata a ci gaba da yada shi ba.
“Ba zai yiwu a ce ana irin wannan kisa a wani yanki na Najeriya ba, kuma sarakuna gargajiya ba su sani ba. In ji shi.
Sarkin, kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya ya ce, Ya roƙi shugabannin ƙasa da su sanya dokoki kan amfani da kafafen sada zumunta saboda illar da suke haifarwa da kuma abubuwan batanci da ake wallafawa game da ƙasa da mutane a cikinsu.
Ya kuma sake jaddada goyon bayan sarakunan gargajiya ga ci gaban dimokuraɗiyya da biyayya ga dukkan shugabannin da aka zaɓa, ciki har da Shugaban Ƙasa, Majalisun Tarayya da na Jihohi, da Gwamnoni.