An sake rantsar da Shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yammacin kasar nan karo na biyu, a matsayin sabbin Shugabannin da zasu ja ragamar jam’iyyar na tsawon shekaru 4 masu zuwa.
Zaben wanda ya gudana a dakin taro na Murtala Square da ke jihar Kaduna, bisa tsarin masalaha wato consensus, inda aka sahalewa Shugabannin da ke jan ragamar jam’iyyar su dora daga inda suka tsaya.
Shugabannin da aka rantsar sun hadar da Muhammad Garba, a matsayin Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma Shugaban jam’iyyar mai kula da shiyyar Arewa maso yamma, sai Isa Sadiq Sakataren shiyyar, da Barrister Bashir Hussaini mashawarci a fannin shari’a, sai Musa mai lafiya Sakataren yada labarai, da Abdulhamid Umar Shugaban matasa, sai Dahiru Gambo a matsayin wakilin masu bukata ta musamman tare da Hajiya Hadiza Alhaji Shugabar mata, sai kuma Salisu Uba Tsafe a matsayin mataimakin Sakatare.
Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana cewa karkashin Jagorancin jam’iyyar su ta APC jihar Kaduna ta samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro, tare da yin kira ga Shugabannin da aka rantsar da su ci gaba da yin jagorancin cikin adalci.
Shi ma a nasa bangaren sabon shugaban jam’iyyar APC shiyyar Arewa maso yamma ya sha alwashin ci gaba da daukar matakan da zasu kara wanzar da nasarar jam’iyyar ta APC.
