
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin gudanar da cikakken aikin tattara bayanai kan adadin makabartu, masallatan Jumu’a da coci-coci da ke fadin jihar, a wani mataki na ƙarfafa tsara ayyuka bisa sahihan bayanai.
A wata sanarwa da shugaban Hukumar Kididdiga ta jihar, Dakta Aliyu Isa Aliyu ya fitar, ya bayyana cewa aikin zai mayar da hankali ne kan tantance yanayin wadannan cibiyoyi ibada da kuma tattara cikakken bayani game da su.
“Wannan aiki na da muhimmanci wajen taimakawa gwamnati wajen samun sahihan bayanan rajistar auratayya da mace-mace, wanda hakan zai taimaka wajen tsara tsare-tsaren ci gaba da suka shafi rayuwar al’umma.
“Aikin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da taswirar cibiyoyin lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, da kuma kidayar makarantun jihar da ake yi a kowace shekara”. In ji shi
Shugaban hukumar ya jaddada cewa wannan mataki wani ɓangare ne na manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na samar da tsare-tsare masu ɗorewa bisa sahihan bayanai.