Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta, cewa tana aikin ƙera makamin nukiliya a ɓoye a cikin jami’ar.
A wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, ƙarƙashin Malam Auwalu Umar, ya fitar, jami’ar ta cecewa labaran da ake yaɗawa ba su da tushe balle makama.
Jami’ar ta ce ta lura da wani faifan bidiyo da na’urar AI ta ƙirƙira, wanda wasu ke yaɗawa suna iƙirarin cewa ABU na ƙera makamin nukiliya a ɓoye.
Zargin dai ya nuna jami’ar da ɓoye aikin uranium tun a shekarun 1980, tare da iƙirarin cewa masu bincike a ABU sun gina injin centrifuge daga Pakistan kuma suna dab da kammala makamin nukiliya a 1987.
Sai dai jami’ar ta bayyana cewa waɗannan zarge-zargen ƙarya ne, domin a wancan lokacin, yawancin masana kimiyyar da ke Cibiyar Binciken Makamashin Nukiliya a Jami’ar (CERT) suna karatu a waje, kuma ba su dawo gida ba sai farkon shekarun 1990.
