Dakarun rundunar sojin kasar nan na Operation HADIN KAI sun kama wani mutum da ake zargin yana da alaka da mayakan kungiyar ISWAP, bayan an same shi da na’urar sadarwar tauraron dan adam ta Star link a karamar hukumar Munguno da ke Jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kama mutumin ne da misalin karfe 3:00 na ranar Laraba a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno yayin da dakarun Bataliya ta 212 ke gudanar da sintiri da kuma binciken ababen hawa.
Rahotanni sunce sojojin sun fara zarginsa ne bayan sun lura da wasu halaye da suka bayyana a matsayin masu tayar da hankali. Bayan binciken kayansa, sun gano na’urar Star link da na’urar Wi-Fi mai tashoshin sadarwa guda shida, wayar hannu da kuma Naira 1,000.
Lokacin da aka tambaye shi, mutumin ya shaida wa jami’an tsaro cewa yana gudanar da kasuwancin samar da intanet a yankinsa, kuma kayan da aka samu a hannunsa na aikin kasuwanci ne.
Sai dai jami’an tsaro sun bayyana cewa yanayin tafiyarsa da irin kayan sadarwar da aka samu tare da shi sun sa ake bukatar ci gaba da bincike. Daga nan aka mika shi tare da kayan da aka kwato zuwa Sashen Leken Asirin Soja na 7 Military Intelligence Brigade (7 MIB) domin gudanar da cikakken bincike.
Masu binciken za su tantance ko mutumin na da alaka da kungiyar ISWAP ko Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS), tare da gano manufar amfani da na’urar Starlink da ko an taba amfani da ita wajen ayyukan ta’addanci ko sadarwar kungiyoyin masu tayar da kayar baya
