Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Jihar Kano ya tabbatar da bullar cutar tun cikin watan Disambar 2024. a Karamar Hukumar Gwale
Sanarwar bullar cutar ya fito ne daga ofishin Babban Jami’in Lafiyar Dabbobi ta Najeriya, a ranar Litinin.
Tana kuma dauke da sa hannun Dakta Taiwo Olasoju, a inda ya ce, cutar murar tsuntsayen tana yaduwa ne a tsakanin kaji da agwagi da zabbi da kuma talotalo.
Sannan ya ce, da kwai babbar barazanar yaduwarta daga Kano zuwa wasu sassan Najeriya.
Don haka ya bukaci gwamnatocin jihohi da ofishin lafiyar dabbobin jihohinsu da su gaggauta daukar matakan da suka dace da kuma bin su sau da kafa domin dakile yaduwar cutar.
Ya kuma bukaci a wayar da kan jama’a da masu kiwo da kuma masu kasuwancin tsuntsaye kan hatsarin cutar da matakan kariya.
Sannan hukumomi su rika sanya ido sosai tare da kai rahoto idan aka ga wata alama ga hukumomin da suka dace.
Aminiya ta rawaito cewa, shugaban Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Jihar Kano, Dakta Usman Gwarzo ya tabbatar da bullar cutar.
“A cikin watan Disambar 2024 wani dalibin sakandare daga unguwar Galadanci a Karamar Hukumar Gwale ya je Kasuwar Janguza da ke Karamar Hukumar Tofa inda ya sayi agwaga ya kai gida ya sanya a cikin kajinsa da yake kiwo a kejin katako.
“Sai agwagwar ta mutu, daga baya kajin suka bi ta, don haka ya kai gawarwakin asibitin dabbobi na Gwale inda aka yi gwajin.
Sakamakon ya fito a ranar 1 ga watan Janairu, 2025. Amma bayan shi ba a samu makamancin hakan ba a wani gidan kaji kuma a Jihar Kano,” in ji Dakta Gwarzo.
Ya ce, kungiyar tana aiki da Gwamnatin Jihar Kano domin wayar da kan jama’a da masu kiwon kaji domin kai rahoton duk inda aka ga alamar cutar ko mutuwar kaji da ba a aminta da shi ba.