Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya sauyawa wasu kwamishinoni da manyan jami’an gwamnatinsa ma’aikatu.
Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya bayyana sauye-sauyen a wata sanarwar da ya fitar da yammacin Litinin.
A cewar sanarwar, babban lauya kuma babban sakataren Ma’aikatar Shari’a, Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad, ya koma Ma’aikatar Muhalli domin ci gaba da aikin Babban Sakatare.
Kwamishinan Harkokin Jin ƙai, wanda ya kasance mai rikon kwarya a Ma’aikatar Sufuri, zai koma babban ofishinsa na asali, wato Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai.
Sanarwar ta kuma ce Gwamna Abba ya umurci dukkan jami’an da aka sauya musu wurin aiki da su mika ragamar aiki ga sabbin shugabanni nan take.
Sauyin zai fara aiki daga yau Talata, 23 ga watan Satumba, 2025.