Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zargi jam’iyyun hamayya da haɗa kai da wasu ƙasashen waje wajen yaɗa labaran bogi cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya.
Wike ya bayyana hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na Channels, inda ya ce waɗannan labaran ƙarya ne da ke nufin bata sunan Najeriya a idon duniya.
Wannan martanin nasa na zuwa ne bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya zargi gwamnatin Najeriya da aikata kisan kiyashi kan mabiya addinin Kirista.
“Kalaman Trump sun dogara ne da siyasa, yana mai jaddada cewa gwamnatin Najeriya ba ta nuna bambanci na addini a cikin ayyukanta.
Matsalar tsaro da ake fama da ita a ƙasar ta shafi Kiristoci da Musulmai baki ɗaya”. In ji shi.
Wike ya kuma kare Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar ba mai tsattsauran ra’ayi bane, domin ya auri Kirista, kuma ya nuna jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mabiya addinai.
