Ƙungiyar Tarayyar Turai ta EU da ECOWASA sun magantu kan zargin da Amurka ke yiwa Najeriya na kisan kiyashi kan Kiristoci.
Kungiyar EU ta ce, ta fahimci cewa ba addini ne kaɗai ke haifar da rikice-rikice a Najeriya ba.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar kan harkokin ƙasashen ƙetare, Anouar El Anouni ya fitar a ranar Talarta.
“Muna jajanta wa mutanen da rikicin ya rutsa da su a Kudanci da Arewa maso Gabashin ƙasar… Akwai abubuwa da dama da ke haifar da rikicin ba addini kaɗai ba ciki har da talauci da siyasa ba”. In ji kungiyar.
-
- Maganar Kisan Gillar Kiristoci a Najeriya ba gaskiya bane – Jakadan Amurka
- Zargin kisan kiristoci: Aikin jam’iyyun hamayya da Ƙasashen Waje ne – Wike
Matakin na ƙungiyar EU na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Najeriya, kan abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ta yi watsi da abin da ta kira iƙirarin ƙarya mai cike da hatsari da shugaban Amurka ya yi cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na far wa kiristoci tare da kashe su a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Talata, ECOWAS ta ce irin wannan barazana ta Shugaba Trump ka iya ta’azzara matsalar tsaro tare da haifar da matsalar zamantakewa a yankin da dama ke fama da matsalar masu tsattsauran ra’ayi.
