Gwamnatin jihar Kano ta kudiri aniyar samar da sabbin matakan tsaro domin dakile matsalolin tsaro da yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar kano, AVM Ibrahim Umar mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar ta’aziya ga iyalan Malam Haruna wanda akai musu gisan gilla a unguwar Chiranchi, dake yankin Karamaar Hukumar Kumbotso.
AVM Ibrahim, ya ce gwamnatin jihar kano ta nuna matukar damuwa game da wannan iftila’in tare da jinjinwa jami’an tsaro bisa namijin kokarin da sukai wajen cafke wadannan batagari cikin kankanin lokaci tare da daukar alwashin hukunta wadanda ake zargin da aikata wannan mummunan aiki.
Kwamishinan tsaron, yace matsalar tsarota shafi kowa a don haka akwai bukatar al’umma su cigaba da bayar da hadin kai ga jami’ai da hukumomin tsaro domin kawar da ayyukan batagari.
