Shugaban hukumar ya ce, Kamen da aka yi masa barazana ce na ya suka daga kan bakansa, amma yana nan daram.
Hukumar Karbar Korafe Korafe Da Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce, babu abin da zai kawo tsaiko a shari’ar tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A hirarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, Muhyi ya yi zargin kamen da aka yi masa a ranar Juma’a barazana ce, kuma ba zai jefa masa tsoron ci gaba da tuhumar Ganduje ba.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na zargin tsohon gwamnan da badakalar biliyoyin Naira a zamaninsa.
Ya ce, tun a shekarar 2021 aka fara binciken shugaban APC na kasa, kuma za a ci gaba da bibiya domin tabbatarwa mutanen Kano adalci.