Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa gwamnati tare da manyan hafsoshin rundunonin tsaro za su kare duk wani soja da yake kan aikin sa bisa doka.
Badaru ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a taron manema labarai na ma’aikatar, wanda aka shirya don bikin tunawa da sojojin da suka mutu wajen kare kasa na shekarar 2026, a ranar Laraba a Abuja.
“To, a ma’aikatar mu, da kuma a cikin rundunonin tsaro gaba ɗaya, za mu ci gaba da kare jami’an mu da suke kan aikin su bisa doka.
“Mun fara bincike a kan wannan lamari, kuma muna tabbatarwa cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka zai samu cikakken kariya.
“Ba za mu yarda a cutar da shi ba muddin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata, kuma muna alfahari da yadda yake aikin nasa,” in ji shi.
Bayanin ministan ya biyo bayan takaddama tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyeson Wike, da wani Laftanar na Rundunar Sojan Ruwa, a ranar Talata kan wata gona da ke Abuja, wadda ake zargin mallakar tsohon Babban Hafsan Sojan Ruwa Vice Admiral Awwal Gambo ce.
Hedikwatar tsaro ta kasa ta goyi bayan jami’in da ya taka wa Wike birki
A wata sanarwa da kakakin rundunar tsaro, Brigadier General Tukur Gusau, ya fitar a ranar Laraba, rundunar ta bayyana cewa, ya na da kima da girma a yi hidima ga Najeriya da gaskiya da mutunci, tare da tabbatar da cewa, jami’an soji suna bin umarni cikin ladabi da ka’ida, ba tare da nuna raini ko tsoro ba.
Batun na zuwa ne, bayan cece-kuce da ya biyo bayan bidiyon da ya nuna Minista Wike cikin muhawara mai zafi da wani jami’in sojan ruwa da ke hana tawagar shiga wani fili da ake rikici a kai.
Ana dai cigaba da duba lamarin a matakin gwamnati da na hukumomin tsaro, domin tabbatar da gaskiya da kuma kaucewa sabani tsakanin ma’aikatu da rundunonin tsaro.
