
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji.
Kakakin Majalisar Abbas Tajudeen ne ya bayyana haka a ranar Talata.
Ya kuma ce, za a gudanar da sauraron ne na wucin-gadi a karkashin kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitoci.
A makon jiya ne ƙudirin dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na biyu.
Zaman sauraron ra’ayin da za a gudanar zai bayar da damar karɓar shawarwarin masu ruwa da tsaki domin ji daga gare su dangane da ƙudirin Dokar Harajin da aka riƙa kai ruwa rana a faɗin ƙasar nan musamman a arewa.
A farkon watan Janairun 2024 gwamnonin kasar nan suka fitar da sabon tsari na rabon haraji a ƙasar, bayan wata gana wa da suka yi da kwamitin da aka kafa domin yin nazari kan ƙudurin sabuwar dokar haraji ta ƙasar.
A ƙarshen shekarar 2024 ce Tinubu ne ya gabatar wa da Majalisun Tarayya ƙudurin aiwatar da gyaran fuska ga dokar harajin, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Wanda hakan ya sa Tinubu da Majalisun Dokokin jingine batun muhawarar da kuma amince wa da dokar har sai bayan an sake yin nazari a kanta.